Ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai a zaɓen 2027.
Tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwar zaman Bashir Ahmad ne ya tabbatar da haka, bayan yaɗuwar jita-jita a kafafen sada zumunta game da shirin Yusuf na shiga siyasa.
A cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Afrilu, wadda aka aika wa masu ruwa da tsaki a mazaɓar Sandamu/Daura/Mai’Adua ta jihar Katsina, Yusuf Buhari ya bayyana shirinsa na tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ya ce: “Ina matuƙar farin cikin sanar da ku aniyata ta tsayawa wannan takara, domin in ba da gudummawa wajen samar da shugabanci nagari da kuma kawo ci gaba ga al’ummarmu.”
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Bashir Ahmad ya ce: “Bayan tuntuba mai zurfi, Yusuf Buhari, ɗan marigayi shugabanmu, ya sanar da masu ruwa da tsaki aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Sandamu/Daura/Mai’Adua a ƙarƙashin APC.”
Tun bayan kammala wa’adin mulkin mahaifinsa, Yusuf Buhari bai cika fitowa a fagen siyasa ba, lamarin da ya sa wannan sanarwa ta zama abin mamaki.
