Wannan na zuwa ne bayan Kwamitin majalisar mai kula da gyaran kundin tsarin mulki ya gabatar da ƙudirin ƙara wasu jihohi 31.
Sabbin Jihohin da ake son karawa su ne New Kaduna da Gujarat daga jihar Kaduna; Sai Tiga da Ari daga jihar Kano, Kainji daga Kebbi; Etiti da Orashi karin kan Jihohi da ake da su a kudu maso gabas, sai Adada daga Enugu, Orlu da Aba daga shiyyar kudu maso gabas.
Sauran su ne Okun, Okura da Confluence states daga jihar Kogi; Benue Ala da Apa daga jihar Benue; FCT state; Amana state daga jihar Adamawa; Katagum daga Bauchi, sai Savannah state daga Borno da kuma jihar Muri daga jihar Taraba.
