Har yanzu fadar shugaban kasa ba ta ce komai ba kan wannan rahoton cibiyar mai fada a ji ta duniya
Shugaba Tinubu ne na uku a jerin mutanen da suka fi iya tsara manyan laifuka da kuma aikata cin hanci da rashawa a duniya
Cibiyar Kula Da Aikata Manyan Laifuka Da Rashawa Ta Duniya (OCCRP) ce ta bayyana hakan a wani rahoto da ta fitar a ranar Talata.
Wannan matsayi sakamakon kada kuri’a ne na wasu fitattun ‘yan jarida da kwararru da kuma wasu daidaikun mutane na duniya wajen zaben mutanen da suka fi aikata tsararrun laifuka a bangaren cin hanci da rashawa a duk shekara.
Tinubu ne ya zo na uku a wannan shekarar 2024, yayin da tsohon Shugaban Syria Bashar al-Assad ya zo na daya. Shugaban kasar Kenya William Ruto ya zo na biyu bayan ya samu kuri’a sama da 40,000 a zaben.
Shugaban kasar Equatorial Guinea ya samu tambarin “rashin tabuka komai a kasarsa” duk ya kasancewarsa shugaban da ya fi kowa dadewa a kan mulki a duniya. Inji rahoton