Tsohon shugaba Joe Biden da ya kamu da wani nau’in cutar Kansar Mafitsara da ya yadu zuwa cikin kashinsa,
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a ranar Lahadi.
A ranar Juma’a ne aka gano cewa Biden mai shekara 82, yana dauke da ciwon kansar bayan ya fara fuskantar matsaloli wajen yin fitsari tare da gano wani ƙullutu a cikin marar sa, in ji sanarwar.
A mafi yawan lokuta, ana iya samun ƙwayoyin cutar kansa a marar maza masu shekaru irin na Biden, amma sau da yawa cutar ba ta yaduwa da sauri.
Maganin hormone na daga cikin hanyoyin jinya da ke hana ci gaban ciwon da rage girman ƙullutun, kodayake ba ya warkar da cutar gaba ɗaya.
A cewar sanarwar, an gano cewa cutar da ke damun Biden na a mataki na 5 wanda shine mafi muni a fannin kimiyya, in ji Hukumar Kansa ta Amurka.
Biden ya bar ofis a watan Janairu na wannan shekarar a matsayin shugaban kasa mafi tsufa a tarihin Amurka, kuma ya sha fuskantar tambayoyi dangane da lafiyarsa da kuma shekarunsa a lokacin mulkinsa.
