Marigayin Tsohon minista ne kuma na hannun daman Sani Abacha a zamanin mulkin soja ne.
Sanarwar rasuwar ta fito ne daga ofishin Dakta Gyang Bere, Daraktan Yada Labarai da Huldar Jama’a, a ranar Alhamis.
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya kuma tabbatar da rasuwar.
Tsohon ministan ya rasu yana da shekaru 82. A cewar sanarwar
Marigayin ya taba zama Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ANPP da kuma wakilin Mazabar Filato ta Kudu a Majalisar Dattawa karkashin PDP a shekarar 2015.
Ya kuma yi gagarumin tasiri a siyasar Najeriya.