
Shugban Amurka Donald Trump ya sanar da tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Iran wanda Netanyahu ya amince hakan a bainar jama’a a farkon makon nan.
A ranar Talata wasu manyan jami’an Iran da hukumomi, ciki har da shugaban ƙasar suka tabbatar da samun sanarwar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin da Isra’ila ta soma da Iran
Sai dai har yanzu, shugaban Addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei bai ce komai ba kan batun tsagaita wutar.
Khamenei ne ke da ikon yanke hukunci na ƙarshe kan muhimman al’amuran ƙasa, kuma har yanzu da dama na jira su ji mai za ce game da yarjejeniyar tsagaita wutar.
Rahotanni sun bayyana cewa Khamenei ya bar matsuguninsa da ke tsakiyar birnin Tehran, inda yanzu yake zama a wani na daban mai tsaro, sai dai Iran ba ta tabbatar da hakan ba.
Ba a sake ganin Khamenei a bainar jama’a tun bayan harin da Isra’ila ta kai Iran a ranar 13 ga Yuni ba.
Rahotannin na cewa kasashen biyu na ci gaba da kai wa juna hari dauk da sanarwar ta shugaban Amurka