
Shugaban Amurka Donald Trump ya mika sakon taya murna ga sabon Fafaroma yana mai cewa wannan babban abin alfahari ne ga kasar.
Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na dandalin sada zumunta jim kadan bayan sanar da nadin Kardinal Francis da fadar Vatican ta yi a yammacin ranar Alhamis.
“Ina taya murna ga Kadinal Robert Francis Prevost da aka zaba a matsayin Fafaroma. Wannan babban abin farin ciki ne da kuma daukaka ga kasarmu. Ina mai fatan haduwa da Fafaroma Leo na 14. Na tabbata haduwar za ta yi matukar alfanu”. In ji shugaba Trump
Fadar Vatican ce ta sanar da Kadinal Robert Prevost a matsayin sabon fafaroman da zai maye gurbin Fafaroma Francis wanda ya rasu a kwanan nan bayan da manya-manyan limaman cocin su 180 suka gudanar da zaben.
Francis shi ne fafaroma na farko daga ƙasar Amurka wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya kuma na 267 a jerin wadanda suka hau wannan kujera.
Sabon Fafaroman zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin, wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan a tarihin cocin.