Ya fadi hakan ne yayin ganawarsa da sarki Abdallah na Jordan, duk da suka da kudurin hakan ke samu daga kasashen duniya.
Shugaban Amurka ya jaddada aniyarsa ta kwashe Falasɗinawan ne zuwa ƙasashen Jordan da Masar, ya kuma fadi hakan ne ga sarki Abdallah na Jordan wanda ya ziyarce shi a Washington a farkon makon nan.
“Ina da yakinin cewa za su samu fili a ƙasashen Jordan da Masar inda za’a kai Falasɗinawan da za a kwashe su daga Gazar.
“Bayan kammala tattaunawar da muke yi, za’a samu wurin da za’a aje Falasɗinawan dake Gaza da za su zauna cikin farin ciki”. In ji shuagaban.
A nasa jawabin kan sarkin na Jordan ya bayyana cewar ƙasarsa za ta kwashi ƙananan yara 2,000 daga Gaza zuwa Jordan, ya kara da cewar Masar za ta gabatar da shirin da suke da shi dangane da makomar Gazar.
Sarkin ya kuma ce, akwai wani taron shugabannin kasashen Larabawa da Saudi Arabia za ta jagoranta wanda zai kunshi kasashen su duka domin daukar matsayin bai ɗaya.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewar kashi 74 na Amurkawa ba sa goyan bayan wannan shiri na Trump wanda zai raba Falasdinawa daga Gaza.
Rahotanni sun ce ƙasashen Jordan da Masar na fargabar rasa tallafin kudaden da suka saba samu daga Amurka domin gudanar da harkokin su na yau da kullum idan suka bijirewa shirin na Trump.
