
Kungiyar rajin tabbatar da adalci ta Transparency International Transparency International hadin gwiwa da cibiyar CISLAC ta nuna damuwa game da cin hanci da rashawa a sashin tsaro na kasar nan.
Kungiyar ta ce cin hanci da rashawa babbar matsala ce a bangare wanda zai iya gurgunta karfinta na magance barazanar tsaro.
Babbabn Daraktan Kungiyar Auwal Musa Rafsanjani ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da kungiyar ta kira, ya bayyana cewa, bangaren tsaro muhimmin bangare ne na tsaron kasa, kuma ya zama wajibi a magance illar cin hanci da rashawa da ke barazana ga tasirin sa.
Da take jawabi bayan taron guda daga cikin masu ruwa da tsaki na taron Maryam Ahmad Abubakar ta ce an gudanarda wannan zaman ne domin tattaunawa da samar da ingataccen bayan ikan yadda za a dakile matsalar cin hanci da rashawa a bangaren tsaron kasar nan. Daga bisani kungiyar ta bayar da shawarwarin inganta gaskiya da rikon amana a harkokin tsaron Najeriya, ciki har da karfafa sa ido a majalisar dokoki da inganta hanyoyin samun bayanan da suka shafi tsaro