
Kasashen biyu sun riƙa yi wa juna musayar wuta da manyan makaman atilari tun daga sanyin safiyar yau Laraba
Indiya ta ce ta ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a kan wurare cikin Pakistan, a matsayin ramuwar-gayya ta harin da wasu ’yan bindiga suka kai yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikonta a watan da ya gabata — wanda a lokacin aka kashe fararen hula 26.
Kafafen yaɗa labarai na Pakistan sun bayar da rahoton jerin fashe-fashe a wurare daban-daban ciki har da birnin Muzaffarabad, da har wutar lantarki ta ɗauke.
Mutane sun mutu a dukkan ɓangarorin, saboda a yayin da Pakistan ta ce harin Indiya ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla takwas, a nata ɓangaren, Indiya ta ce fararen hula 3 sun mutu a kusa da Kashmir sakamakon harba manyan makaman atilari da Pakistan ta yi.
Wani jami’in gwamnatin Indiya, Azhar Majid ya ce, Indiyawa 8 ne suka mutu, kana 29 suka samu rauni a wannan Laraba a garin Poonch na Kashmir, kusa da iyaka da Pakistan.
Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Asif ya ce, an harbo jiragen yaƙin India biyar kuma an yi garkuwa da sojojin India takwas a matsayin fursunonin yaƙi.
Tun da farko, Ministan Watsa Labaran Pakistan Attaullah Tarar ya shaida wa TRT cewa an harbo jirgi guda ɗaya a birnin Akhnoor da ke yankin Kashmir wanda ake taƙaddama a kansa.
Sannan aka harbo wani jirgin a birnin Ambala na ƙasar Indiya, kazalika an harbo jirgi marasa matuƙi a lardin Jammu na ɓangaren Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya.
Tarar ya ƙara da cewa sojojin Pakistan sun mayar da martani ne kan harin da India ta kai ƙasar da makamai masu linzami waɗanda ta harba a yankunan “fararen-hula.”
Wani mai magana da yawun rundunar sojojin Pakistan ya ce sun “lalata” wasu kayayyakin tsaron India.
Mai magana da da yawun majalisar dinkin duniya ya ce, babban sakataren majalisar, António Guterres, ya damu matuka kan wannan tsakanin India da Pakistan, kuma ya yi kira ga kasashen biyu da su kai zuciya nesa.
Shugaba Donald Trump na Amurka cewa ya yi yana fatan za a gaggauta kawo karshen rikicin tsakanin kasashen biyu masu makamin nukiliya, makwabtan juna.
Ya ce, ” abin kunya ne yanzu muka ji labarin a daidai lokacin da muke shigowa wannan ofis. Mun ji labarin yanzu,. Ina ganin mutane sun san wani abu zai faru, bisa la’akari da dan abin da ke tsakaninsu a baya.
Sun dade suna yaki da juna. Tsawon gomman shekaru da karni suna yaki, idan ka duba. A’a, ina fatan zai kare cikin sauri.” In ji shi.
Zaman tankiya tsakanin kasashen biyu ya tsananta ne tun bayan harin watan da ya gabata, inda India ke zargin Pakistan da mara baya da ‘yan ta’adda da ke kai hari yankinta – zargin da Pakistan ta musanta.
Indiya da Pakista sun sha gwabza faɗa tun bayan kafa su a shekarar 1947 da Turawan Birtaniya suka yi.