Daga Safinatu Abdullahi
An fara aikin titin tun zamanin mulkin Buhari amma aka yi watsi da shi, rashin kyawaun hanyar na hallaka da haifar da matsalar sufuri a cewar al’ummar yankin,
Al’ummar garin Rimin gado da Kanye da kuma Garo da ke Karamar Hukumar Kabo sun koka kan rashin kammala aikin titi da ya dauko tun daga Kano zuwa Dayi da ke iyakar Katsina.
Mazauna garuwan da titin ya ratsa sun bayyana damuwar su da yadda gwamnati ta yi watsi da aikin dake da matukar muhimmanci ga al’ummar yankin.
Wakilinmu da ya rawaito cewa, a halin yanzu, ma’aikata sun barje titin an kuma rarraba shi, wanda hakan ke kawo matsala a wajen sufuri da kuma dakile kasuwancin mazauna yankin.
Mutanen da aka yi hira da su sun ce yadda aka bar aikin a halin yanzu, ya na jawo masu matsaloli fiye da saukin da aka sa ran zai kawo a lokacin da aka soma shi.
“Babban abin da yak e bamu tsoro shi ne yadda rashin kyan hanyar ya ke lakume rayukan matafiya da na mazauna garin”. Inji wani magidanci a garin.
Mutanen yankin da Premier radio ta yi hira da su, sun yi kira da gwamnati da taimaka ta kammala aikin hanyar.
An fara aikin wannan titi ne tun lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari, amma mazauna garin sun bayyana cewa ‘yan kwangilar sun kwashe komai na kayan aikinsu daga yankin, an kuma bar su a cikin mawuyacin hali.