
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Sanata mai wakiltar yankin Kano ta Arewa Barau Jibril Maliya, ya bayyana daga darajar kwalejin Fasaha ta Kabo zuwa Jami’ar kimiyya da fasaha ta gwamnatin Tinubu a matsayi babban tagomashi ga al’ummar jihar.
Sanatan ya bayyana hakan ne jawabinsa a wani biki na musamman a yayin taron bude jami’ar da aka gudanar a harabarta dake garin Kabo a ranar Talata.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawaan ya kuma bukaci alummar jihar Kano da na arewacin Najeriya da su yi amfani da damar da suka samu daga shugaban kasa, ta
“Samar da wannan jami’a dama ce ga ‘yan Kano da Arewa da ma kasa baki daya, har da ‘yan kasashen waje na su ci gajiyarta wajen karatu.
“Kuma hakan zai bunkasa tattalin arziki da darajar da jihar Kano ke da ita. Wanda hakan ya kara yawan jami’o’in gwamnati tarayya a jihar Kano daga biyu zuwa guda uku.
Sanata Barau ya kuma kara da cewa samun wannan jami’a wata karin dama ce wajen diban ma’aikata ‘yan asalin jihar masu kananan sana’o’I da za ta taimaka wajen bunkasa musu sana’ar ta su.