
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa Majalisar Kasa kan tabbatar da dokar ta-ɓaci da ya ayyana a Jihar Ribas, yana mai cewa sun nuna kishin ƙasa ta hanyar ajiye bambancin siyasa don magance matsalar tsaro.
A wata sanarwa da kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, Tinubu ya ce wannan mataki na da nufin wanzar da zaman lafiya da warware rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar tsawon kusan watanni 15.
Shugaban ya bayyana cewa rikicin Jihar Ribas ya tsananta har yana barazana ga kadarorin man fetur da kuma tattalin arzikin ƙasa, lamarin da ke iya haifar da cikas ga manufofin gwamnatinsa na bunƙasa tattalin arziki.
Tinubu ya ce amincewar Majalisar Dokoki da dokar ta-ɓacin wata shida na nufin ba wa gwamnatin riƙo damar daidaita al’amura tare da samar da sulhu tsakanin ɓangarorin da ke rikici a jihar.

Haka kuma, ya gode wa ‘yan Najeriya bisa fahimtar da suka nuna, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da su ba shi goyon baya don tabbatar da zaman lafiya a Jihar Rivers.
Sai dokar na ci gaba da samun suka daga ‘yan adawa da kungoyin masu zaman kansu da kuma Kungiyar lauyoyi ta kasar. Suma mai cewa, dokar da Tinubu ya yi amafani da ita tsohuwa ce kuma babu ita a sabon kundin tsarin mulki na 1999.