Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya zabebben shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama murnar lashe zaɓen da aka gudanar
Shugaban ya yi hakan ne ta wayar tarho ga sabon shugaban mai jiran gado.
Tinubu ya yi fatan sabon wa’adin na Mahama zai ƙara kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da kuma yankin Yammacin Afirka.
Shugaban ya kuma yaba wa ’yan Ghana bisa gudanar da zaɓen da suka yi cikin kwanciyar hankali, wanda haka alama ce ta dorewar dimokuraɗiyya kasar.
Sannan ya kuma jinjina wa ɗan takarar jam’iyyar mai mulki, kuma shugaban kasar a yanzu Dokta Mahamudu Bawumia wanda ya sha kaye ya kuma rungumi kaddara.
Tinubu ya jaddada aniyar Najeriya na ƙara danƙon zumunta da Ghana tare da gode wa shugaban ƙasa mai barin gado na irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban ƙasar da zaman lafiya a yankin.shugaban ƙasa da aka
An gudanar da babban zaben na kasar Ghana ne a ranar 7 ga watan Disamba a inda shugaba mai ci ya sha kaye.