Sanarwar ta bayyana cewa Janar Olufemi Oluyede ya maye gurbin Janar Christopher Musa a matsayin sabon babban hafsan tsaro.
Haka zalika Manjo Janar W. Shaibu ya zama babban hafsan soja na kasa.
Sai kuma Air Vice Marshall S.K. Aneke ya zama sabon babban hafsan sojin sama, sai kuma Rear Admiral I. Abbas a matsayin Babban Hafsan sojin ruwa.
A gefe guda kuma Janar E.A.P. Undiendeye zai ci gaba da rike mukaminsa na babban daraktan Leken Asiri.
Mai kuke ganin ya janyo shugaba Tinubu daukar wannanan matakin?
