
Shugaba Bola Tinubu na ziyarar jihar Katsina a yau.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar ya ce, a ziyarar ta kwanaki biyu zai fara ta ne daga yau Juma’a – shugaban zai gana da masu ruwa da tsaki domin nazartar yanayin tsaro a jihar.
Sanarwar ta ce shugaban zai ƙaddamar da cibiyar ayyukan noma ta zamani da wani titi mai hannu biyu, mai tsawo kilomita 24 da gwamnan jihar, Dikko Radda ya kammala.
Bayo Onanuga ya kuma ce, Shugaban zai halarci ɗaurin auren ‘ƴar gidan gwamnan Katsinan kafin kammala ziyarar a jihar.
Tuni gwamnan jihar Dikko Umaru Radda ya ayyana yau juma’a a matsayin ranar hutu domin ma’aikata da sauran al’ummar jihar su samu damar yi wa shugaban kasa tarba ta musamman.