
Naja’atu Muhammad ta zargi shugaban Tinubu da wuce gona da iri wajen cire gwamnan jihar Rivers da kuma mulkin kama-karya a kasar.
Fitacciyar ‘yar siyasa kuma ‘yar gwagwarmaya ta bayyana hakan ne a hirarta da wakilinmu ta wayar tarho a ranar Alhamis.
“Babu dokar da ta ba shugaban kasa ikon cire gwamnan da aka zaba, ba tsige ka aka yi ba kuma ka zama kana fama da matsanancin rashin lafiyar hana gudanar da aiki ba ko mutuwa. In ban da haka babu dalilin da za a canja rantsatstsen shugaba.” In ji ta
‘Yar siyasar wacce ta nuna takaicci da fushinta kan alamarin ta ce, matakin da Tinubu ya yi a jihar Ribas ya yi ne don ya faranta wa Wike wanda yake rigima da zababben gwamna jihar Fubara.
“Me ya sa ba a sa dokar ta baci a jihar Katsina ba a inda dubbannin mutane suke hannun ‘yan ta’adda. Ka duba Sakkwato, ka kuma duba abin da su Turji suke yi. In ji ta.
Shugaba Tinubu yana shan suka kan matakin da ya dauka na sa dokar ta-bacin da kuma cire gwamna Fubara da kuma nada tsohon Babba Hafsan Sojin ruwa a matsayin Kantoma wanda zai gudanar da mulkin jihar.
Naja’atu ta kuma nuna illar sakamakon matakin da Tinubu ya dauka ga rahotannin fashe-fashen bututun mai da yanzu aka soma a jihar wanda hakan zai iya kara durkusar da tattalin arzikin kasar da dogara kan danyen man fetur.