Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar tabbatar da adalci a sha’anin haraji da shugabanci (Tax Justice) ta bukaci kara wayar da kan al’umma kan hanyoyin karbar haraji (KIRS).
Babban jami’I mai kula da shirye-shirye da tsare-tsare na kungiyar Sadiq Muhammad Mustapha, ne ya bayyana haka yayin taron da suka yi kan duba tsararrakin aiki na hukumar haraji (KIRS), ranar Laraba.
Ya ce akwai bukatar hukumar haraji ta Kano ta inganta hanyoyin magance matsalolin masu biyan haraji da kuma basu amsa dangane da kalubalan da suke fuskanta na biyan haraji.
Sai dai Sadiq Muhammad Mustapha, ya ce hukumar tana da kwararrun ma’aikata da kayan aiki wanda hakan yasa suka yaba mata.
Ya kara da cewa tana tabbatar da cewa ta inganta hanyoyin biyan haraji da samar da fahimtar juna tsakanin ma’aikatan da masu biyan haraji.
Ya kuma bukaci (KIRS) ta kara yawan ma’aikatan ta da zasu rinka kula da sha’anin masu biyan haraji.
A nasa bangaren matemaki na musamman ga shugaban hukumar tattara kudin shiga (KIRS) na Kano, Nafi’u Shehu Rikadawa, ya ce taron hadaka ce da kungiyar Tax Justice dake tabbatar da an yiwa masu biyan haraji adalci.
Ya ce sun fahimci inda ya kamata a ce sun gyara da kuma kara kaimi tare da fahimtar guraren da suka yi abinda ya dace.
Nafi’u Shehu Rikadawa, ya ce a jadawalin da suka fitar a baya hukumar tana kasa-kasa sai dai ya ce hukumar ta samu cigaba a sabon jadawalin da Tax Justice din suka fitar.
Ya ce mataki da suka samu na cigaba ya faru ne sakamakon jajircewar shugaban hukumar karbar haraji na Kano Zaiyid Abubakar.