
Tashar wutar lantarki na gwamnatin Kano zai fara aiki a shekarar da mai zuwa.
Kwamishinan ma’aikatar Wutar Lantarki da Samar da Makamashi na Jihar Kano, Dakta Ghaddafi Sani Shehu ne ya bayyana hakan a lokacin ziyarar duba ayyukan da ya kai a tashar da ke Tiga da kuma Challawa.
Kwamishinan ya bayyana jin daɗinsa kan yadda ayyuka ke tafiya, tare da tabbatarwa jama’ar jihar Kano cewa gwamnati ta kuduri aniyar inganta samar da wutar lantarki a fadin jihar.
“Bayan kammala ayyukan, tasoshin za su samar da wutar lantarki mai dorewa tare da ƙarfin samar da wuta daga megawatt 10 zuwa sama.
“Inganta fannin wutar lantarki a Jihar Kano babban ci gaba ne da zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma da kasuwanci a jihar.” In ji shi.
Manajan tashar wutar lantarkin mallakin jihar Kano, Injiniya Ado Ibrahim Doguwa, a jawabinsa ya ce, Kano ce jiha ta farko a Najeriya da ta mallaki nata tashar samar da wutar lantarki ta ruwa.