
Gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta tabbatar da kai hari kan dakarun Pakistan a wurare da dama da ke iyakarsu ta arewaci.
Mai magana da yawun Taliban ya ce, sun kashe dakarun sojin Pakistan 58 a abin da ta kira na ramuwar gayya.
Kasar ta kuma iƙirarin cewa Pakistan ta keta alfarmar sararin samaniyarta kuma ta kai hari a wata kasuwa ranar Alhamis.
Pakistan ta musanta adadin, tana mai cewa sojojinta 23 ne suka mutu a gwabzawar da take yi da mambobn Taliban guda 200.