
Mahukuntan Taliban a Afghanistan sun sanar da rufe dukkan hanyoyin sadarwa a fadin kasar, makonni bayan da suka fara katse intanet, da nufin hana abin da suka bayyana da “tabarbarewar tarbiyya.”
Wata kungiya mai sa ido kan harkokin yanar gizo ta tabbatar da cewa yanzu haka ana fama da cikakken rashin intanet a kasar, lamarin da ya shafi al’ummar da ke dogaro da intanet wajen sadarwa da gudanar da ayyukan yau da kullum.
Wani jami’in Taliban ya shaida wa manema labarai cewa rufewar za ta ci gaba har sai an fitar da wata sanarwa ta daban daga shugabancin kungiyar mai rike da ragamar gwamnatin kasar.
Shugaban Taliban, Hibatullah Akhundzada ne ya bayar da umarnin katse layukan sadarwa na intanet da ke karkashin kasa tun a farkon wannan wata.
A cewar rahotanni da Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ya rasa damar samun sadarwa daga ofishinsa na Kabul ciki har da wayar salula, lamarin da ke ƙara tabbatar da tsananin rufe hanyoyin sadarwa a kasar.