Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce talauci da koma bayan tattalin arziki ne manyan abubuwan da suka haifar da masaloli tsaro a yankin arewacin Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan a cikin shirin siyasa na gidan talibijin na Channels.
Ya yi gargaɗin cewa muddin ba a magance su gaba ɗaya ba to yankin zai ci gaba da fuskantar matsalolin tashe-tashen hankalin.
“Fiye da kashi 60 zuwa 65 cikin 100 na mutanen arewacin Najeriya – musamman a shiyar arewa maso yamma – na fama da tsananin talauci a lokacin da ya zama gwamman jihar Kaduna. hakan na iya sa matasa da dama su shiga aikin ta’addanci kasancewar ƴan bindiga za su iya ɗaukar su haya domin kai hare-hare”. In ji shi.
Gwamnan ya kuma ce, gwamnatinsa ta soma ne da fito da hanyoyin yaƙi da talauci da rashin aikin yi tsakanin matasa.
