
Wani rahoton bankin duniya ya ce har yanzu talauci na cigaba da ƙaruwa a Najeriya duk da sauye-sauyen tattalin arziƙin da Gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa domin farfado da tattalin arziƙin ƙasar.
Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ne ya bayyana haka a Abuja wajen kaddamar da rahoton cigaban da ake samu a kasar nan.
“Aƙalla mutane miliyan 139 ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci a shekarar 2025… Duk da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ɗan bunƙasa, kuma gwamnati tana samun ƙarin kuɗaɗen shiga, yawancin jama’a har yanzu na fama da tsadar rayuwa da wahalhalu.” In shi.
A gefe guda, bankin ya yaba wa Najeriya bisa ƙoƙarin da take yi wajen daidaita farashin musayar kuɗaɗen waje da rage giɓin kasafin kuɗi.
Sai dai ya ce waɗannan nasarori ba su kawo sauƙi ga rayuwar jama’a ba.
Jami’I bankin ya shawarci gwamnati da ta rage hauhawar farashin kayan abinci, ta kuma yi amfani da kuɗaɗen jama’a yadda ya kamata, kuma ta faɗaɗa shirin tallafa wa marasa ƙarfi.
Rahoton, ya yi hasashen cewa tattalin arziƙin Najeriya zai iya bunƙasa zuwa da kashi 4.4 cikin ɗari nan da shekarar 2027, ta hanyar bunƙasar noma, da masana’antun da ba su da alaƙa da harkar man fetur.