
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin kafa Hukumar Kula Da Harkokin Addinai, bayan gabatar da rahotanni da kuma amincewa da su a zaman majalisar.
Shugaban kwamitin majalisa kan harkokin addinai, Naziru Abubakar ne ya gabatar da rahoton kwamitin kan kudirin Kafa hukumar kula da harkokin addinai, wanda majalisar zartarwa ta gabatarwa majalisar inda nan take majalisar ta amince da kudirin.
“Za a kafa hukumar ne domin ta zama wata hanya ta hana rikice-rikicen addini, da karfafa zaman lafiya da fahimtar juna da kuma karfafa dangantaka tsakanin gwamnati da kuma kungiyoyin addinai”. In ji shi.
Majalisar ta Kuma amince da kudirin dokar Kafa hukumar asusun tallafin noma domin inganta harkokin noma da zuba jari a fannin noma a jihar ta Kaduna.
Majalisar ta kuma karbi rahoton bukatar Kafa hukumar Kula da harkokin a gwangwan a jihar.