Gwamnan Adamawa ya yi watsi da korar da PDP ta yiwa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike daga jam’iyyar.
PDP ta kori Wike da Sanata Samuel Anyanwu da tsohon Gwamnan Ekiti Ayodele Fayose a yayin babban taronta da aka gudanar a ranar Asabar a Ibadan babban birnin Jihar Oyo.
A sanarwar da Gwamna Fintiri ya fitar, ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyar ta ɗauka, domin hakan zai ƙara haifar da rikici a cikin jam’iyyar.
“Ina son na bayyana a fili cewa ba na goyon bayan korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Wike daga PDP. Wannan mataki ba zai amfani jam’iyya ba.
“Na yi imani cewa sulhu da fahimtar juna su ne hanyar da ta fi dacewa. Ina kira ga kowa ya yi aiki don ganin an samu haɗin kai a cikin jam’iyya. In ji shi.
Gwamnan ya ce, yana fatan ganin zaman lafiya da haɗin kai su ɗore a jam’iyyar, ya kuma ’ya’yan jam’iyyar da su mayar da hankali kan yin sulhu maimakon ƙara haddasa rikice-rikice.
Fintiri na cikin gwamnoni huɗu da suka halarci taron, kuma shi ne Shugaban Kwamitin Shirya Taron.
Gwamnonin Jihar Osun, Ademola Adeleke; Taraba, Agbu Kefas; da Ribas, Siminalayi Fubara ba su halarci taron ba.
