
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya cika alkwarin Naira miliyan 15 na jinya ga Halisa Muhammad tsohuwar ‘yar Kannywood mai fama da ciwon sankarar mama.

Gwamnan ya cika alkawarin ne ta hanyar aika wa da kudin ga asusun maras lafiyar domin cigaba da yi mata magani kamar yadda ya yi alkawari.

Halisa Muhamma ta sha fama da larurar sankarar mama da tsananin da ta kai ga neman taimakon jama’a a shafukan sada zumunta har gwamna Abba Kabir Yusuf ya gani.
A watan da ya wuce ne gwamnan ya tura wakili gidan maras lafiyar don ganin halin da ke ciki, ya kuma yi alkawarin taimaka wa.
Halisa Muhammad na daya daga cikin tsaffin jaruman finafinan Hausa kuma a yanzu daya daga cikin dattawan masana’antar .