
Sojojin Sudan a fadar shugaban kasar cike da murnar kwace birnin (Hoto: BBC)
Khartoum, babban birnin Sudan da aka ragargaza a yanzu ya kasance shiru, bayan tsawon makonni da aka ɗauka ana artabu da sojin gwamnati da kuma dakarun RSF.
Khartoum, cibiyar kasuwanci da fadar gwamnatin ƙasar, yanzu ya zama kufai.
Sake karɓe iko da babban birnin ƙasar wata babbar nasara ce a yaƙin basasar ƙasar da aka shafe shekaru biyu ana yi, wanda ya faru sanadiyyar son mulki tsakanin shugaban sojojin kasar da kuma shugaban dakarun RSF.

Yar jaridar BBC ta shiga birnin kwanaki kaɗan bayan da sojojin Sudan suka sake karɓe iko daga hannun dakarun RSF bayan shafe watanni shida suna bata-kashi kan kwatar birnin.
Girman abubuwan da aka lalata a tsakiyar Khartoum ba zai misaltu ba: an lalata ma’aikatun gwamnati da bankuna da ofisoshi – sun ƙone ƙurmus, sun koma launin baki.
Filin jirgin saman birnin ya zama kufai ga jirage da aka rugurguza, wuraren duba fasfo da kuma kayayyaki a cikin filin jirgin ya koma toka.

A fadar shugaban ƙasar, Wuri ne mai muhimmanci ga mayaƙan na RSF wanda dakarun RSF suka mamaye tun soma yaƙin shekaru biyu da suka wuce .
Wurin ya cika da ɓaraguzai da kuma gilasai da suka farfashe.
Kura ta turnuke kujerun da a baya ake amfani da su wurin shirya manyan taruka, an sace tare da lalata komai – har wayoyin lantarki ma an cizge su daga jikin bango.
Kadan kenan na irin barnar da ido ke iya gani.
Wannan shi ne yaƙin basasar Sudan na uku cikin shekara 70, a ɗaya gefen, shi ne mafi muni kan saura da aka samu – saboda sauran yaƙe-yaƙen an yi su ne a wasu sassan ƙasar a dubun-dubatar mutane suka tsere.
Ga ‘yan wadanda suke Khartoum, da Allah ya sa suka tsira da rayukansu,sun yi murnar kawo karshen baƙin mamayar RSF.

“Ina jin kamar an sake halittata ne,” a cewar Osman al-Bashir, wanda mazaunin birnin da yakin ya dai-daita, a bayyanin da yake na irin wahalar da suka sha.
“Dakarun RSF sun sace komai a birnin wanda kuma sojoji suka yi wa ƙawanya – ga kuma dakatar da ka agaji da Amurka ta yi. Ana fama da matsalar ƙarancin abinci, amma akwai fata mai kyau yanzu”. In ji shi.
“Ina jin daɗi. Ina cikin kariya, duk da cewa ina jin yunwa,” a cewar wani dattijo, mai suna Kasim Agra.
“Ka sani, ƴanci shi ne abin da yafi muhimmanci. “Kamar yadda kake gani, ina ɗauke da wayata,” in ji shi, ya faɗa tare da nuna waya cikin aljihunsa.
“Ba za ka iya riƙe waya ba makonni biyu da suka wuce.” In ji dattijon da Allah Ya yiwa gyadara dogo.
Wannan shi ne abin da mutane da dama a wasu sassan Khartoum suka faɗamin – wayoyin salula na da muhimmanci, kuma shi ne abin da mayaƙan RSF ke hari don sacewa.

Mista Agra yana cike da fatan cewa Khartoum da kuma ƙasar Sudan za su farfaɗo.
“Ina tunanin gwamnati za ta kawo masu zuba jari daga: Amurka da Saudiyya da Canada da kuma China, za su sake gina wannan ƙasar, na yi imanin haka.”
Ko da an sake gina waɗannan wurare da aka lalata, zai yi wuya a sake ganin irin wuraren tarihi da birnin Khartoum ke da su a baya.
Mata da dama sun bayyana cewa a yanzu za su sake komawa yin barci kamar a baya, bayan shafe tsawon lokaci a farke cikin dare sakamakon fargabar cewa mayaƙan RSF za su far musu.
Girman fargaba da kuma asara ba zai misaltu ba: akwai labarai daban-daban na cin zarafi da kuma rayuka da aka salwanta.