
daga ƙauyen Lilo a ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
Al’ummar kauyen sun yi zaman makokin rasuwar sojojin, waɗanda suka rasa rayukansu yayin artabu da yan bindiga. Yan bindiga sun kashe sojoji biyar da wasu yan kasuwa
Mai magana da yawun al’ummar da ƙauyuka maƙwabta, Mohammed Mohammed, ya ce harin ya faru a farkon mako a kan hanyar Lilo zuwa Gulubba yayin da sojoji ke raka yan kasuwa zuwa kasuwar Gusau.
Shaidu sun ce yayin da yan bindigar da suka ɓoye a gefen hanya tare da fitowa su fara harbi, yawancin yan kasuwar sun gudu cikin daji, domin tsira da rayukansu.
Sai dai maharan sun kashe sojoji biyar da yan kasuwa kusan 10.
Al’ummar sun roƙi gwamnati a matakan ƙananan hukumomin, jiha da tarayya su tallafa musu wajen tsaro, ilimi, lafiya da samar da hanyoyi.
Kakakin sojojin, Kyaftin David Adewusi, ya ce bai san da labarin harin ba amma zai yi bayani daga baya.