Sojojin Najeriya karkashin Operation HADIN KAI (OPHK) sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda tare da hallaka sama 50 daga cikinsu.
Hakan na kunshe ne a cikin a wata sanarwa da rundunar ta fitar, mai dauke da sa hannun Kakakin rundunar hadin gwiwa na operation Hadin Kai a Arewa Maso Gabas, Laftanar Kanar SANI UBA a ranar Alhamis.
Rundunar ta ce, ‘yan ta’addar sune suke kai hari a wurare daban-daban a yankin Arewa maso Gabas, ta kuma yi arangama da su ne a yayin da suka kai hari kan sansanonin sojoji da ke Dikwa, Mafa, Gajibo (duk a Jihar Borno,
karkashin Sashe na 1) da kuma Katarko (Jihar Yobe, karkashin Sashe na 2).
“ ‘Yan ta’addan sun kai hare-haren ne a lokaci guda, amma sojoji sun tsaya daram, suka yi jajircewa da ƙwarewa wajen kare matsayinsu, tare da fatattakar dukkan maharan.
“An samu cikakken nasara bayan jiragen yaki na rundunar sojin sama da ke ƙarƙashin Operation Hadin Kai (OPHK) sun kai hare-haren sama masu daidaito a kan maboyar ’yan ta’adda.
“An samu wannan nasarar ne ta hanyar amfani da bayanan leƙen asiri, sa ido da na’urorin ISR da na’urorin ISR, wanda ya ba sojojin ƙasa damar ganin duk abin da ke faruwa a fagen daga tare da samun damar kai martani cikin ƙarfi da inganci.
“Haɗin gwiwar dakarun ƙasa da na sama ya kai ga kashe fiye da ‘yan ta’adda 50, tare da kwato makamai masu yawa, ciki har da bindigogi 38 nau’in AK-47, manyan bindigogi 7 PKT, bututun RPG guda 5, GPMG guda 2, gurneti da kuma dubban harsasai iri daban-daban”. In ji sanarwa.
Hedikwatar Sojojin Najeriya ta yaba da jarumta da jajircewa da kuma sabuwar himma da dakarun suka nuna.
Sannan ta jaddada cewa hakan ya sake tabbatar da ƙudurin sojojin Najeriya na kare iyakokin ƙasa da tabbatar da zaman lafiya a duk fadin kasar, musamman bayan ƙarin sojoji da kayan yakin zamani da aka tura zuwa yankin.
Rundunar hadin gwiwar ta Operation HADIN KAI na ci gaba da gudanar da ayyukan kai farmaki da tsaurara tsaro a yankin Arewa maso Gabas, domin tabbatar da cewa ‘yan ta’adda ba su sake samun mafaka a cikin ƙasar nan ba, a cewar sanarwar.
