Sojojin Najeriya da ke aiki a ƙarƙashin rundunar Operation Fansar Yamma, sun samu nasarar kashe ƙasurgumin ɗan bindigar nan Dan Dari Biyar, a lokacin wani aiki da suka gudanar a yankin Sabon Birni na jihar Sokoto.
Wata majiyar soji ce ta tabbatar da kisan ɗan bindigar da aka yi a ranar Alhamis, lokacin da yake ƙoƙarin amsar kuɗin fansan wasu mutane da ya yi garkuwa da su.
Samamen da sojoji suka kai ya kasance na haɗin gwiwa ne tsakaninsu da ƴan sa kai da ke ƙarƙashin gwamnatin Sokoto, inda suka samu nasarar kwato makamai da alburusai da kuma na’urorin sadarwa.
Shi dai Dan Dari Biyar ya yi wanda ya yi kwaurin suna lokacin da ya ce yafi mutunta naira ɗari biyar kan ran mutum, ya jagoranci kai hare-hare a ƙauyukan Lalle da Tsamaye da Gidan Sale da kuma wasu yankuna na Gwadabawa da Gwaronyo.
Haka nan wasu bayanan jami’an tsaro sun alaƙantashi da kai hare-hare a yankunan da ke gabashin jihar ta Sokoto.
