
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Sudan ya ce sojoji sun ƙwace iko da Khartoum babban birni kasar daga hannun dakarun RSF.
Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna Janar Abdel Fattah Al-Burhan ya sauka a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa da ke birnin wanda sojoji suka ƙwace iko da shi.
A inda da saukarsa ya fadi yayi sujudar godiya ga Allah da wannan nasara da suka samu na kwace birnin bayan da ‘yan tawayen suka fatattake su a shekarar 2023.
“Yanzu birnin na Khartoum ya kuɓuta daga hannun abokan gaba”. In ji shugaban cikin murna.
Rahotanni sun ce sojojin na samun nasara cikin sauri tun bayan da suka karɓe iko da fadar shugaban ƙasar a farkon makon nan.

An kuma ga fararen hula na yin murna kan titunan birnin.
Sai dai dakarun har yanzu dakarun na RSF ne aka ce ke iko da yawancin yankin Dafur.