
An shiga zaman dar-dar a birnin Fatakwal yayin da motocin yaƙi na sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Jihar Ribas.
Hakan na zuwa jim kaɗan ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.
An hangi motoci motocin soji 10 aka hanga suna sintiri a kan hanyar zuwa gidan gwamnatin yayin da wasu motocin yaƙi masu sulke suka tsaya wuri-wuri a hanyar.
Majiyar ta ce titunan birnin na Fatakwal sun zama fayau a yayin da mazauna suka tsere gidajensu.
Babu tabbaci ko gwamnan da aka dakatar Similanayi Fubara yana cikin gidan gwamnatin a halin yanzu.
Sai dai majiyoyi sun ce akwai yiwuwar gwamnan ya samu labarin cewa za a ayyana dokar ta ɓacin tun kafin faruwar lamarin.
Bayanai sun ce gwamnan ya shafe tsawon wunin wannan rana ta Talata yana ganawa da ’yan majalisar zartarwarsa.
Aminiya ta rawaito cewa, a halin yanzu birnin na Fatakwal ya zama fayau a yayin mazauna da ’yan kasuwa duk sun koma gidajensu.