
Sojojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP 15 a wani mummunan hari da suka kai a Ngamdu, karamar hukumar Kaga ta jihar Borno.
wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwar Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar ya ce ‘yan ta’addan sun kai harin ne da manyan bindugu samfurin RPG, da jiragen yaki marasa matuki da kuma bama-baman kirar (IEDs) domin kai hari kan sojoji da motocinsu.
Saidai duk da tsananin harin, sojojin sun tsaya tsayin daka wajen mayar da martani da karfin wuta, wanda ya jawo mummunar asarar rayuka ga ‘yan ta’addan.
sanarwar ta tabbatar da cewa an kashe ‘yan ta’adda 15 yayin musayar wuta, yayin da sojoji hudu suka rasa rayukansu, kuma wasu biyar suka jikkata.
Harin ya kuma yi sanadiyar lalacewar wasu motocin yakin sojojin.
A cewarsa, ‘yan ta’addan sun yi yunkurin hana isowar taimako ta hanyar dasa bama-bamai a hanyar dake hade Ngamdu da Damaturu saidai rundunar ta bada tabbacin tono duka bama-bamai uku da binciken su ya binciko bayan murkushe harin kuma tuni aka bude hanyar.