
Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kama mutune 69 da ake zargi da hannu a fasa-kaurin mai tare da kwace sama da lita 32,000 na danyen man fetur da aka sace a yayin wani sumame da aka gudanar a sassa daban-daban na Neja-Delta.
A cikin sanarwar da Lt. Colonel Danjuma Jonah Danjuma, mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na Shiyya ta 6 ya fitar a Fatakwal ranar Lahadi.
Ya ce aikin ya gudana ne tsakanin 11 zuwa 24 ga Agusta, 2025, tare da haɗin gwuiwar sauran jami’an tsaro, inda aka lalata gudanar da haramtattun wuraren tace mai tara.
A jihar Delta, an cafke manyan motoci guda biyu dauke da sama da lita 15,000 na man da aka tace ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Sapele, inda aka kama mutum uku da ake zargi da hannu.
Sanarwar ta ce duk mutanen da aka kama an mika su ga sauran hukumomin tsaro domin gurfanar da su a kotu, yayin da kayayyakin da aka kwace aka sarrafa su bisa tsarin aikin dakarun.