Sojojin sun kuma ceto mutane 249 da aka yi garakuwa da su duk watan Janairun wannan shekara.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta kasar ta fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar wacce Daraktan Yada Labaran Hedikwatar Manjo Janar Edward Buba ya sa wa hannu ya kuma ce, sojojin sun kama mutane 59 da ake zargi da satar mai tare da ceto mutum 249 da aka yi garkuwa da su a yankin kudu maso kudu.
Edward Buba ya ce, dakarun sun dakile satar mai da ya kai na fiye da Naira biliyan 2, sun kuma kwato makamai 370 da harsasai sama 4000.
Kakakin ya kuma ce, dakarun za su cigaba da yaki da ‘yan ta’adda a faɗin kasar domin samar da yanayin tsaro ga ‘yan kasa.