
Kungiyar Malaman Jami’oi ta Kasa ta tsunduma yajin aikin gargadi na mako biyu.
Umarnin da uwar kungiyar ta baya ya nuna cewa daga daren Lahadi mambobin kungiyar sun ajiye aiki a wani mataki na gargadin gwamnatin kan abin da suka kira karya alkawura da gwamnatin tarayya ta sha yi a musu a baya.
A martaninta na yajin aiikin, Gwamnatin tarayya ta yi barazar kin biyan albashin duk malamin jami’ar da ya shiga yajin aikin, abin da ake gani zai kara dagula lamurra.
Ministan Ilmi Tunji Alausa a cikin wata sanarwa da ya fitar a Lahadin, ya isar da matayin gwamnatin tarayya kan lamari.
ASUU kuma ta ce, barazanar hakan ba wani sabo abu bane, kuma babu gudu, babu ja da baya.