
Shugabannin tsaron kasashen Afirka 54 na taro yau Litinin a Abuja domin tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro da suka addabi nahiyar.
Ana gudanar da taron ne a karkashin jagorancin Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa.
Janar Musa ya ce taron, wanda shi ne irinsa na farko, zai bai wa shugabannin soji na Afirka damar tattauna matsalolin tsaro a fili tare da tsara hanyoyin magance su ba tare da dogaro da kasashen waje ba.
Ya kuma ce taron zai duba batun rundunar sojin hadin gwiwar kasashen Afirka wadda har yanzu ba ta samu cikakken tsari ba, saboda matsalolin kudi da tsare-tsare.
Fiye da kashi 90 cikin 100 na kasashen da aka gayyata sun tabbatar cewa za su halarci taron, kazalika manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya da tsoffin hafsoshin tsaro da kwararru a harkokin tsaro za su halarta.
Christoper Musa ya ce burin taron shi ne ganin nahiyar Afirka ta samu tsaro da kuma ci gaba.