
Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano REMASAB Ambasada Ahmadu Haruna Zago ya rasu
An sanar da rasuwar ce a safiyar Alhamis bayan fama da rashin lafiya.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan hukumar ne ta tabbatar da rasuwar Ahmadu Haruna Zago a asibiti.
A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2023 Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa Haruna Zago a matsayin Shugaban Hukumar REMASAB