Shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar, Birgediya Janar Abdourahamane Tchiani ya bayyana aniyarsa na aiwatar da shawarwari da matakan da aka cimma a babban taron ƙasa.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairu, inda ya ce zai duba tare da nazarin matakan da aka ɗauka a taron.
Babban taron ƙasar ya yanke hukuncin bai wa Janar Tchani wa’adin shekara biyar a matsayin shugaban mulkin riƙon ƙwarya, tare da ba shi damar tsayawa takara bayan Nijar ta koma tsarin dimukuraɗiyya.
Shugaban ya nanata cewa za a bai wa manyan batutuwa muhimmanci, musamman haƙo albarkatun ƙasa da muhalli da tsaro da mulki da ilimi da kuma alaƙar Nijar da ƙasashen duniya.
Janar Tchani ya kuma jaddada cewa babban taron ya samar da tsari mai inganci na komawa ga mulkin dimukuraɗiyya da tsarin tafiyar da ƙasar nan gaba.
