
Shugaban Majalisar da Sanata Natasha a wani zama na majalisar
’Yar Majalisar Dattawa daga Jihar Kogi Sanata Natasha Akpoti ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio da neman yin lalata da ita.
‘Yar majalisar ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da tashar talabijin ta Arise a safiyar Juma’a.
Sanatan ta ce, tun da ta ki amincewa da buƙatar Shugaban Majalisar ya kafa mata ƙahon zuƙa a zauren majalisar.
Ta kuma kara da cewa, mijinta ma shaida ne a kan yunkurin Akpabio ne yin lalata da ita.
Aminiya ta rawaito cewa, a hirar da aka yi da ita, Sanatan ta ce, tana da hujjoji da hotunan saƙonnin da Shugaban majalisar ya aika mata.
“Akpabio ya sha kirana ta manhajar WhatsApp”. In ji ta.
Natasha ta kuma buƙaci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bibiyi wayar da suka yi domin gano gaskiya.
A makon da ya gabata ne Natasha ta yi wa Akpabio wankin babban bargo a zauren Majalisar bayan ya sauya mata kujera ba tare da tuntubar ta ba.
Shugaban majalisar ya ba da umarnin ne bayan da ’yan majalisar suka kada ƙuri’ar amincewa da hakan, domin tabbatar da dokokin zauren Majalisar.
Daga bisani ya tura lamarin ga kwamitin ladabtarwar majalisar ta gudanar da bincike tare da gabatar da rahoto cikin makonni biyu.
Ana cikin haka ne ’yar majalisar ta maka shi a kotu tana neman diyyar Naira biliyan 100.03.
‘Yar majalisar ta bayyana cewa ta sha neman gabatar da kudiri kan Masana’antar Mulmula Karfe ta Ajaokuta a zauren Majalisar amma Akpabio yana kin sanya batun a jerin abubuwan da za a tattauna a majalisar.
Bayan ta nuna damuwarta wasu sanatoci suka bukaci ta je ta yi masa magana saboda muhimmancin masana’antar.
“Da na yi masa magana sai ya ce, “Sanata Natsaha, a matsayina ba shugaban majalisar nan, Ni ke da wuƙa da nama. Ya kamata kin ki ki ba ni kulawa, domin idan kika kuka da ni za ki samu alherai masu yawa.” Inji ta.
Ta ce, ko da ta bayyana masa cewa ba ta fahimta ba sai ya ce, “ya rage naki.”
Ta kuma ce, “wannan abun da ke faruwa da ni daidai yake da na malamin da ke wahalar da ɗalibarsa saboda ta ƙi kwanciya da shi.”
Ta bayyana cewa tun a shekarar 2023 Akpabio ya fara yi mata wannan mummunan tayi a lokacin da ita da mijinta suka ziyarce shi domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Ta ce “yana rike da hannuna muna zagayawa yana nuna mana cikin gidansa, mijina na biye da mu, sai ce zai soma ce na zo gidansa mu huta.
“Mijina da ke biye da mu ya ji maganar, saboda haka ya hana mu tafiya ƙasar waje ni kadai ko in yi tafiya da Akpabio shi kadai.”
Zuwa yanzu dai babu wani martani daga Akpabio dangane da wannan zargi, a yayin da batun ke ta yawo a kafofin sada zumunta.