Kudurin dokar da ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattijai na shan suka musamman daga arewacin kasar
Rahotanni na cewa fadar shugaban kasa na shirin janye dokar haraji dake gaban majalisar dattijai saboda cece-kuce da matsin lambar kudurin musamman daga arewa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, wasu majiyoyi masu tushe sun tabbatar mata cewa shugaban kasa na shirin janye kudirin, biyo bayan shawarar Majalisar Tattalin Arziki.
Majalisar ta zauna karkashin Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a ranar Asabar, a inda ta sake ba da shawarar janye kudirin.
Sai dai an ce, akwai wasu bangarori da za a sake yi wa kwaskwarima domin sake mayar da kudurorin dokokin gaban majalisa
Gwamnonin Arewa 19 da sarakunan gargajiya na yankin sun yanke shawarar yin watsi da kudurin a wata ganawa da suka yi a Kaduna cikin watan Oktoba.
Shima tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi kira ga majalisar dattijai da ta saurari ra’ayin al’umma kan batun sabon kudirin kafin zartar da shi.