
Shugaban Amurka Donald Trump ya sauka a ƙasar Saudiyya a ziyararsa ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya a wa’adinsa na biyu a matsayin shugaban Amurka.
Tuni shugaban ya sauka a Riyadh babban birnin kasar a jirgin saman Air Force One na shugaban Amurka ya kuma samu tarba daga Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman kafin su wuce fadar Al Yammaman domin ganawa ta musamman.
Shugaba Trump ya yi zaman farko da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, kafin su shiga wani zaman sirri a fardar gwamnatin Saudiyya.
Kafin nan, shugaba Trump ya gana da Mohammed bin salman da Sakataren harkokin waje, Marco Rubio a filin jirgin sama na sarki Khalid da ke Riyadh.