Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Daddiyar Daular Larabawa ta Dubai a daren Lahadi domin halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week na shekarar 2026, wanda zai mayar da hankali kan ɗaukar matakan kare sauyin yanayi da kuma bunƙasa ci gaba mai ɗorewa a duniya.
Shugaban kasar wanda ya samu tarba daga Ministan Harkokin Wajen na Ƙasa, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan da Jakadan kasar nan a Dhabi Salem Saeed Al-Shamsi da Ministan Harkokin Wajen Najeriya
Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da kuma jami’an ofishin jakadancin Najeriya da ke Abu Dhabi.
A yayin taron na kasa da kasa ana ran shugaban kasa Tinubu zai gaba da wasu daga cikin shugabannin kasashen duniya da suka hada da Shugaban Rwanda, Paul Kagame, da kuma Shugaban Faransa, Emmanuel
Macron domin ƙarfafa alaƙar bunƙasa tattalin arziƙi, da kuma tattauna muhimman ƙalubalen yankuna da na duniya baki ɗaya.
Taron Abu Dhabi Sustainability Week na 2026 zai buɗe a hukumance a yau Litinin, inda Shugaba Tinubu zai kasance tare da sauran shugabannin ƙasashe da manyan masu ruwa da tsaki na duniya domin tsara matakai masu amfani da za su kai ga cimma makomar fitar da hayaki mai gurbata muhalli.
