
Jama’ar Kano na bayyana mabanbantan ra’ayi dangane da shirin hawan Sallah da Sarkin Muhammadu Sanusi II da kuma Sarki na 15, Aminu Ado Bayero ke shirin gudanarwa a bikin salla na wannan shekara.
A hirar da wakilinmu ya yi da wasu mutane kan yadda suke ganin hawan na bana, sun nuna fargabar abin da ka je ya zo dangane da tsaro a yayin bikin na sarakunan biyu a gari daya.

Ra’ayin Jama’a
“Ni ba za ni ba, bana kuma fatan wani nawa ya je. Amma muna fatan a samu abin da ake so ta fuskar tsaro da kuma zaman lafiya a jihar Kano…. Al’amuran nan dai abin dubawa ne”. In ji wani mutumin da bai fadi sunansa ba.
“Mafi sauki shine a hakura da wannan hawan idan har zai kawo cikas ga zaman lafiyar jihar Kano, saboda a shekarun baya a lokacin bullar cutar Korona sallar Juma’a kacokam aka hana, to, in dai abin da ake so a samu zaman lafiya, hankalin kowa ya kwanta”…. In ji wani magidanci a hirar.
Jaridar Aminiya a shafinta na intanet ta rawaito irin wannan fargarbar a wani rahotonta na hirar da ta yi da wasu mutanen Kanon don ta bakinsu dangane da hawan Sallah da sarakunan biyu ke shirin yi.
Malam Haladu Bello, wani dattijo mai shekaru 78 a duniya, ya bayyana damuwarsa kan cewa lamarin zai iya haifar da rikici.
“Na sha ganin hawan salla mai ƙayatarwa da kuma wanda ke da matsaloli, amma wannan yana da ban tsoro. Abin takaici ne yadda shugabanninmu ke watsi da hatsarin da jama’a ke fuskanta.” In ji shi.
Wani matashi kuma mai shekaru 30, Alhaji Usman Shehu, ya bayyana cewa wannan rikicin cikin gida ne, ba wai abu ne da zai sa mutane cikin fargaba ba.
“Kullum cikin fargabar abin da zai biyo baya muke. Wannan ba daidai ba ne. A bar mu, mu more al’adunmu cikin zaman lafiya.”

Matsayar ‘yan sanda
A waje daya kuma, Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce, a shirye take ta tunkari da kuma magance duk wata matsalar tsaro a yayin bikin, kuma za ta ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kan batun hawan.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin gamayyar kungiyar masu zaman kan su karkashin jagoranci Dakta Musa Sufi da kuma shugaban kwamitin kyautata alaka tsakanin al’umma da ‘yan sanda bisa jagorancin Ambasada Ali Hassan Bayero a ofishinsa a ranar Talata.
“Rundunar ‘yan sandan Kano ta shirya gudanar da ayyukanta tare da sauran hukumomin tsaro domin a kare lafiya da kuma dukiyoyin al’umma.
“Mun tanadi jami’an da ake da bukata domin dakile duk wata barazanar tsaro a lungu da kuma sakon dake fadin jihar Kano. In ji kwamishina Bakori.
Daukacin Jama’ar Kano na fatan ganin an wanye lafiya dangane da wannan bikin sallah, la’akari da muhimmacin hawan daba a bukukuwan sallah a Kano da kuma yadda hawan ya samu daukakar da Hukumar Kula da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta sa shi a cikin jerin ababen tarihi na duniya.

Danbarwar sarautar Kano
Danbarwar sarautar ya fara ne bayan da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe Muhammadu Sanusi na II daga sarauta, tare da naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.
A shekarar 2024, Majalisar Dokokin jihar ta sake sauya dokar masarautar tare da rushe dukkannin masarautu biyar da Ganduje ya ƙirƙira ta kuma mayar da Sanusi a matsayin Sarki.
Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce da tashin hankali a jihar, lamarin da ya sanya tsagin Aminu Ado Bayero tafiya kotu.
Kotu ta yanke hukuncin cewa kowa ya tsaya inda yake kan wannan batu, har zuwa lokacin da Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci na ƙarshe, lamarin da ya sa dukkanin ɓangarorin biyu ke iƙirarin suna da iko a kan sarautar.