Ahmad Hamisu Gwale
Shirin AGILE da ke tallafawa karatun Mata, da ke samun goyan bayan bankin Duniya da maaikatar ilimi a Kano, sun horar da wasu daga cikin Malaman makarantun jihar dabarun koyar da yara masu bukata ta musamman da nufin karfafa musu gwiwa.
Shugaban shirin AGILE a nan Kano, Malam Mustapha Aminu, ya bayyana horar da Malaman makarantun zai basu damar kara inganta koyarwar su, wanda hakan zai taimaka wajen inganta karatun yara masu bukata ta musamman.
Mustapha Aminu, ya kuma ce shirin AGILE ,tuni ya fara yunkurin kai dauki ga makarantun masu bukata ta musamman a Kano, farawa da makarantar Tudun Malika da ke nan Kano.
Taron bitar na kwana guda, ya gudana a dakin karatu na Murtala Muhammad da ke State Library, a yunkurin shirin AGILE na ci gaba da bai wa bangaren ilimi kulawar da ta kamata domin bunkasa harkokin koyo da kuma koyarwa a makarantun jihar Kano.
A jawabinsa a yayin bitar, Dakta Auwalu Inuwa Bello, na sashen ilimin koyarwa na masu bukata ta musamman daga jami’ar BUK, ya gabatar da mukala kan rawar da ilimi ke takawa ga ci gaban zamani.
Haka zalika itama Dakta Samira Ali, daga sashen ilimin masu bukata ta musamman daga kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, ta karfafa bukatar bai wa ilimin masu bukata ta musamman kulawa domin amfanuwar al’umma.
Shi kuwa Nasiru Yakubu, wanda malami ne a sashen ilimin masu bukata ta musamman daga jam’ar BUK, ya gabatar mukala na yadda al’adu marasa kyau ke kawo ci kas ga ilimin masu bukata ta musamman.
Taron bitar na kwana guda,a ya samu halartar bangarori da dama daga fannin ilimi, kuma ya samu goyan bayan shirin SPIU, da kungiyar iyayen daliban makarantu da kwamitin SBMC da sauransu.
