Kasancewar a yau lahadi ne yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra’ila zai soma aiki.
Palasdinawa fursunoni 1,650 za su shaƙi iskar ’yanci daga gidajen yarin Isra’ila.
Sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin Hamas da Isra’ila da zai fara aiki karfe 6.30 na safiya.
Isra’ila za ta sako tarin Palasdinawa da take tsare da su wadanda ba su ji ba su gani ba.
Yayin da kuma Hamas za ta sako mutane 33 daga cikin waɗanda ta kama a Isra’ila a harin ranar 7 ga Oktoba, 2023 a matsayin kashin farko na yarjejeniyar.
Bangarorin biyu sun amince za a yi musayar ne a bisa adadin da suka yarda a tsakaninsu a yayin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a ranar Laraba a Qatar