Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan wata sabuwar doka ta musamman da za ta rage farashin haƙo mai da iskar gas a Nijeriya.
Wannan mataki na da nufin jawo sabbin masu zuba jari, da kuma ƙara fadada hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na Gwamnati.
Dokar, wanda ake kira ‘Dokar Taimako Don Rage Farashin Ayyukan Mai Da Iskar Gas, ta 2025’, za ta ba da gudummawar haraji ga kamfanonin Mai da gas wanda suka rage farashin ayyukansu bisa ƙa’idojin masana’antu. Kamfanonin da suka cimma waɗannan mataki za su iya samun kashi 50% na ƙarin kuɗin da Gwamnati za ta samu daga rage farashin.
Duk da haka, gudummawar harajin ba za ta wuce kashi 20% na harajin da kamfani ke biya a shekara ba, domin tabbatar da daidaito tsakanin taimakon masu zuba jari, da kuma kula da kuɗin shigar Gwamnati.
Hukumar kula da mai da Iskar Gas ta Nijeriya (NUPRC) za ta fitar da ƙa’idodin farashi na shekara-shekara don ayyuka daban-daban kamar a ƙasa, da ruwa mai zurfi, da tekun zurfi.
Za a kuma fitar da cikakkun bayanai game da wannan dokar a cikin ƴan makonnin nan. Gwamnati ta yi imanin cewa wannan dokar za ta ƙara inganci a fannin mai da iskar gas.
