
Kungiyar SERAP ta gurfanar da Hukumar Rarraba Kuɗaɗe da Tsare-tsare ta kasa (RMAFC) gaban kotu kan shirinta na ƙarawa manyan jami’an gwamnatin Tarayya albashi, ciki har da shugaban ƙasa da mataimakinsa da gwamnoni da mataimakansu da kuma ‘yan majalisa.
A watan da ya gabata ne hukumar ta kare wannan shiri tana mai cewa albashin da waɗannan jami’an ke samu a yanzu “baya isarsu.”
“Gyaran albashin ya dace, kuma ya yi daidai da yanayin tattalin arziki da ƙasar nan ke ciki”. In ji hukumar.
A ƙarar da SERAP ta shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta kalubalanci ingancin shirin.
Kungiyar ta roƙi kotu da ta bayyana wannan ƙarin albashi a matsayin abin da ya sabawa doka da tsarin mulki, kuma ba ya kan ka’ida kamar yadda Kundin Tsarin Mulki na 1999 da dokar RMAFC suka tanada.
SERAP ta kuma nemi kotu da ta umurci RMAFC ta rage albashi da alawus na shugaban ƙasa, mataimakinsa da gwamnoni da mataimakansu da kuma ‘yan majalisa, domin ya dace da halin matsin tattalin arziki da ‘yan Najeriya da dama ke ciki a yanzu.