Senegal ta zama zakarar Gasar Nahiyar Afirka ta 2025, bayan doke mai masaukin baƙi, Maroko da ci ɗaya mai ban haushi a wasan ƙarshe na gasar.
Ɗan wasan tsakiyar Senegal, Pape Gueye ne ya jefa ƙwallo ɗaya tilo a raga a minti na 94, bayan shafe minti 90 ba tare da zura ƙwallo ba.
Ƙwallon tasa ta bai wa ƙasarsa damar sake lashe gasar a karo na biyu a tarihinta.
Wasan dai ya ɗauki zafi lokacin da alƙalin wasa ya bai wa Maroko bugun fenariti a minti na 96, daf da tashi daga wasan.
Hukuncin ya janyo taƙaddama lamarin da ya sanya kocin Senegal bai wa ’yan wasansa umarnin ficewa daga filin.
Sai dai ɗan wasan gaban Maroko Brahim Diaz ya ɓarar da fenaritin, inda mai tsaron ragar Senegal Edourd Mendy ya kama ƙwallon.
’Yan wasan ƙasar Senegal sun koka kan yadda alƙalin wasan ya jagoranci wasan, inda suka yi zargin ya yi wa masu masaukin baƙi alfarma.
