
Daga Fatima Muhammad Aliyu
Gwamnatin jihar Kano ta kare batun sayen Motocin alfarma ga bangaren masarautun jihar.
A hirarsa da Wakiliyarmu, Kwamishinan Yada Labarai na jihar Abdullahi Wayya ya ce, sayen motocin ba laifi bane, hasali ma hakan biyayya ne ga tsarin doka da kuma bai wa masarautun damar aiwatar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali don amfanar al’umma.
“Da akwai bukatar al’umma su kara fahimta cewa motocin na hidimtawa alumma ne ba na sarakunan na kashin kansu bane, ba ba kuma kyauta bane na tsakanin mutum da mutum. Kayan gwamnati ne.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa, “Sarkin Kano Muhammadi Sunusi na II ma’aikacin gwamnati ne kuma al’umma yake yi wa hidima, yana da hakki na kayan aiki ko kuma duk abubuwan da yake bukata na samar da kayan aikin don gudanar da aikinsa a masarauta a tanadar masa a matsayinsa na wanda aka dora wa hidima ta al’umma.
A farkon makon nan ne aka yi ta yayata wata takardar umarnin fitar da Naira Miliyan 15 kowannensu daga asusun kananan hukumomin jihar 44 wanda jimlar kudin ya kai Miliyan 670 don saya wa sarkin Kano motocin alfarma wanda hakan ya janyo ce-ce ku ce a shafukan sada zumunta da kuma ‘yan adawa.
Rahotanni sun ce sama da shekara biyu sarkin yana amfani ne da motoci na kashin kansa ne da kuma tsaffi tun na zamanin sarki Ado Bayero